Sin na maraba da karin baki da su yi yawon bude ido a kasar
2024-07-17 19:33:12 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na maraba da karin abokai ‘yan yawon bude ido, dake son zuwa kashe kwarkwatar ido a dukkanin sassan kasar, da wurare masu kayatarwa dake cikin kasar.
Lin Jian, ya bayyana hakan ne a Larabar nan, lokacin da yake tsokaci game da yadda ziyarar rukunin jama’a ke kara samun karbuwa a kasuwannin yawon bude ido na kasa da kasa.
Rahotanni na cewa, a baya-bayan nan, ana matukar kara samun masu sha’awar ziyartar kasar Sin domin yawon shakatawa, wanda hakan wani tagomashi ne da Sin din ke samu a kasuwannin yawon bude ido na kasa da kasa. Wasu kamfanonin shirya tafiye-tafiye na kasa da kasa ma na cewa a bana, adadin baki ‘yan kasashen waje dake neman ziyartar kasar Sin ya linka har rubi 4 kan na shekarar bara.
Game da hakan, Lin Jian ya ce Sin na ci gaba da goyon bayan harkokin musayar jama’a tsakaninta da takwarori na kasashen waje, inda al’ummun kasashe 15 irinsu Faransa, suka shiga tsarin gwajin ziyartar kasar Sin ba tare da Biza ba na tsawon kwanaki 15, kana Sin ta fadada aiwatar da tsarin ba da izinin yada zango ba tare da Biza ba, har na tsawon sa’o’i 144 ga al’ummun wasu kasashe, a wasu tasoshin shiga kasar ta Sin da aka kara adadinsu zuwa 37.
Tuni dai kasar Sin ta fara aiwatar da cikakken tsarin shiga ba Biza, ga baki masu yawon bude ido na rukunonin jama’a, wadanda suke cikin jiragen ruwa na yawon shakatawa, kana tana aiwatar da tsarin kyautata hidimomi masu nasaba da hakan, irinsu biyan kudade ta wayar salula, da sayen tikiti a wuraren da suke ziyarta cikin kasar ta Sin. (Saminu Alhassan)