Hadin kan gabashi da yammacin kasar Sin na taimakawa ci gaban yankunan karkarar garin Minning dake jihar Ningxia
2024-07-17 17:13:51 CMG Hausa
Tun kusan shekaru 20 da suka gabata, har zuwa yanzu, ana kokarin fadada hadin-gwiwa daga fannoni daban-daban tsakanin garin Minning dake gundumar Yongning a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta ta kasar Sin, da lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar, al’amarin da ya samar da ci gaba sosai ga yankunan karkarar garin, har ya zama abun misali ga hadin-gwiwar gabashi da yammacin kasar Sin ta fuskar yaki da fatara.