logo

HAUSA

Sin a shirye take ta shiga tsakani domin cimma maslaha tsakanin bangarorin Falasdinawa

2024-07-16 19:28:04 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kasar a shirye take, ta samar da dandali, da damammaki na cimma daidaito tsakanin sassan Falasdinawa dake da sabani da juna.

Da yake tabbatar da hakan a Talatar nan, kakakin ma’aikatar Lin Jian, ya jaddada cewa, har kullum Sin na goyon bayan warware takaddama, da dunkulewar sassan Falasdinawa ta hanyar gudanar da shawarwari. Jami’in ya yi tsokacin ne a matsayin martani, ga rahotannin dake cewa, wasu manyan jami’ai daga tsagin kungiyar Fatah da na Hamas, za su iso birnin Beijing a karshen mako mai zuwa domin ganawa da juna. Ya ce, za a fayyace dukkanin bayanai game da hakan a lokaci mafi dacewa.

Lin ya kuma ce, Sin da sauran bangarorin Falasdinu na aiki tukuru wajen cimma nasarar hakan, yayin da kuma Sin ta shirya karfafa tattaunawa, da tsare-tsare tare da daukacin sassa masu ruwa da tsaki, don hada karfi da karfe da nufin cimma maslaha, tsakanin bangarorin Falasdinawan dake da sabani da juna.    (Saminu Alhassan)