logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin a rabin farkon bana ya nuna sakamako mai kyau

2024-07-16 20:58:34 CMG Hausa

Game da alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar kan tattalin arzikin Sin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana a yau Talata cewa, yawan GDPn kasar a rabin farkon shekarar bana ya zarce kudin Sin yuan triliyan 60, wanda ya karu da kashi 5 cikin dari, bisa na makamancin lokaci na bara, kana ya nuna cewa, Sin ta samu sakamako mai kyau a wannan fanni. Duk da fuskantar matsin lamba, kuma yayin da ake fama da rashin tabbaci kan tattalin arzikin duniya, tattalin arzikin Sin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da karuwar tattalin arzikin duniya.

Lin Jian ya bayyana cewa, tattalin arzikin Sin yana da tushe, da karfi da kyakkyawar makoma, kuma an kiyaye bunkasarsa yadda ya kamata a dogon lokaci, da tabbatar da samun ci gaba mai inganci, da kuma ci gaba da bude kofa ga kasashen waje.

Jirgin kasa na 10,000 da zai yi jigila a tsakanin Sin da Turai a shekarar bana ya tashi daga birnin Wuhan a kwanakin baya, kwanaki 19 kasa da irin wannan mataki da aka cimma a shekarar bara.

Game da hakan, kakakin ya bayyana cewa, jerin jiragen kasa dake jigila a tsakanin Sin da Turai, jeri ne dake dauke da kaya masu ratsa sassan Sin da Turai, kana suna kawo kyakkyawar damar samun ci gaba. A nan gaba kuma, jerin jiragen kasan za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da yin mu’amala, da samun moriyar juna, da hadin kan kasa da kasa, don samun bunkasuwa mai inganci cikin lumana, da sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya, da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya baki daya. (Zainab Zhang)