Shugaba mai ci na Rwanda na da rinjaye a zaben da ake gudana
2024-07-16 10:54:30 CMG Hausa
Kwamiti mai kula da harkokin zabe na kasar Rwanda ya ba da sakamakon kididdigar kuri’u da aka kada a zaben shugaban kasar a daren jiya Litinin, a cikin kashi 79% na kuri’un da aka riga aka kidaya, shugaba mai ci Paul Kagame ya samu kashi 99.15%.
An dai fara zaben shugaban kasa da na majalisar wakilan kasar Rwanda a jiya, an kuma kammala kada kuri’ar zaben shugaba a yammacin wannan rana, inda za a kawo karshen zaben majalisar a yau Talata.
An kada kuri’a a zagaye daya ne kawai bisa tsarin zabe na kasar, kuma wanda ya samu rinjaye shi ya lashe zaben.
Bisa labarin da mahukuntan kasar suka bayar, an ce, za a gabatar da sakamakon zaben a mataki na farko kafin ranar 20 ga wannan wata, daga bisani za a samu sakamakon karshe kafin ran 27 ga wannan wata. (Amina Xu)