logo

HAUSA

Kasuwar hayakin carbon ta kasar Sin tana da karko

2024-07-16 10:44:00 CMG Hausa

Yau 16 ga wata ne aka cika shekaru uku da kaddamar da kasuwar cinikayyar hayakin carbon ta kasar Sin. Ya zuwa ranar 15 ga watan Yuli, yawan cinikin da aka samu na kason iskar carbon a kasuwar carbon ta kasar Sin ya zarce tan miliyan 460, tare da hada-hadar cinikin kusan yuan biliyan 27. Gaba daya aikin kasuwar na cikin kwanciyar hankali, kuma yana sa kaimi ga kamfanonin samar da wutar lantarki wajen kiyaye muhalli.

Yadda yawan farashin ciniki na hayakin carbon yake, haka yawan farashin da kamfanonin za su biya a lokacin da suke sayan kason iskar carbon.

Kasuwar carbon ta kasar Sin, wata babbar sabuwar hukuma ce wadda ke amfani da hanyoyin kasuwanci don sarrafawa da rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma mai kiyaye muhalli, kuma muhimmin makami ne na manufofin inganta iskar carbon a kololuwa da tsaka tsakin matakai. Kana ta zama wata muhimmiyar taga ga kasar Sin don mayar da martani sosai kan sauyin yanayi. (Yahaya)