An kaddamar da zama na 3 na kwamitin kolin JKS na 20
2024-07-15 14:06:29 CMG Hausa
A yau Litinin, kwamitin kolin JKS karo na 20 ya kaddamar da zaman taronsa na 3 a nan birnin Beijing.
Sakatare janar na kwamitin kolin Xi Jinping, ya gabatar da rahoton aiki a madadin ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tare da bayani kan daftarin kudurin kwamitin kolin na kara zurfafa gyare-gyare da inganta zamanantar da kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)