logo

HAUSA

Masu horar da Kongfu na Sin sun taimakawa Nijar horas da ’yan wasan da za su halarci gasar Olympics ta matasa ta Dakar

2024-07-15 15:38:07 CMG Hausa

An yi mu’amala da cudanya tsakanin masu horar da wasan Kongfu na Sin, da ’yan wasan Kongfu da masu sha’awar wasan na kasar Niger, a Niamey fadar mulkin kasar, daga ran 8 zuwa 13 ga watan nan. Niger ta kasance zango na biyu da aka kafa dandalin mu’amalar fasahar Kongfu da shirin horas da ’yan wasan Kongfu na Sin da Afrika, matakin da zai taimakawa kasar horas da ’yan wasan gasar Olympics ta matasa ta shekarar 2026 da za a gudanar a Dakar na kasar Senegal.

Shugaban kungiyar wasan Kongfu ta kasar Nijar Amadou ya ce, ziyarar rukunin masu horas da fasahar Kongfu na Sin ba shaida bunkasuwar huldar kasashen biyu kadai ta yi ba, har ma da zama wata gada ta inganta mu’ammalar al’adun bangarorin biyu.

Yayin ziyararsu, masu horo na Sin sun horar da nau’o’in Kongfu daban daban, matakin da ya amfanawa ’yan wasan Kongfu da masu sha’awarsa fiye da 300, wajen inganta kwarewarsu.

Jakadan Sin dake kasar Jiang Feng ya bayyana cewa, Kongfu wata fasaha ce ta al’adun kasar Sin, kuma a shekarun baya-baya nan, ya kara samun karbuwa a Niger, kana mu’ammalar da aka yi a wannan karo a bangaren Kongfu ya taka rawar gani wajen kara tuntuba game da al’adun kasashen biyu tsakanin jama’arsu. (Amina Xu)