logo

HAUSA

Sin ta fadada manufar yada zango a kasar ba tare da biza ba zuwa karin tashoshi

2024-07-15 11:01:16 CMG Hausa

Hukumar kula da shige da fice ta kasar Sin ta sanar a yau Litinin cewa, an fadada tsarin yada zango a kasar na sa’o’i 144 ba tare da biza ba zuwa karin tashoshi guda uku, lamarin da ya kai adadin tashoshin kasar da manufar ta shafa zuwa 37.

Sanarwar ta ce, sabbin tashoshin guda uku sun hada da filin jirgin sama na kasa da kasa na Zhengzhou Xinzheng dake lardin Henan na kasar, da filin jirgin sama na kasa da kasa na Lijiang Sanyi dake lardin Yunnan na kasar, da tashar jirgin kasa ta Mohan dake lardin Yunnan.

A halin yanzu, 'yan kasashen waje daga kasashe 54 suna da damar yin amfani da wannan tsarin yada zango a kasar ba tare da biza ba na sa'o'i 144. A wannan lokaci na zama ba tare da biza ba, masu yawon bude ido na da damar yin ayyuka na gajeren lokaci kamar tafiye-tafiye da ziyarar aiki. (Yahaya)