logo

HAUSA

Sin ta sanyawa wasu kamfanoni da Amurkawa da suka sayarwa Taiwan makamai tarnaki

2024-07-15 20:32:38 CMG Hausa

Game da batun cewa Amurka ta sayarwa yankin Taiwan makamai, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kasar Sin ta dauki matakan sanya tarnaki ga wasu kamfanonin Amurka, da manyan shugabanninsu, da kuma kamfanonin samar da makamai da suka shiga aikin sayarwa Taiwan makamai, da baiwa Taiwan din damar halartar dandalin tattaunawa kan sha’anin kiyaye tsaro a tsakanin yankin na Taiwan da kasar Amurka.

Bisa labarin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayar a ranar 12 ga wannan wata, Sin ta dauki matakan ne kan kamfanonin samar da makamai na Amurka 6, da manyan shugabannin kamfanonin 5.

Lin Jian ya bayyana cewa, batun yankin Taiwan batu ne dake shafar muhimmiyar moriyar kasar Sin, kana shi ne batu mafi muhimmanci yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Ba za a kyale duk wata kasa, ko kungiya, ko mutum ya illata matsayin Sin da jama’arta wajen tabbatar da ikon mallakar kasa, da cikakkun yankunan kasar ba. Kana bai kamata a tsoma baki cikin harkokin yankin Taiwan ba. (Zainab Zhang)