‘Yan kasuwan ketare za su samu sabbin damammaki a kasar Sin
2024-07-15 20:58:50 CMG Hausa
Alkaluman hukumar kididdaga ta kasar Sin (NBS), sun nuna a yau Litinin cewa, yawan GDPn kasar Sin ya karu da kaso 5% a farkon rabin shekarar nan ta 2024, idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. Kaza lika karuwar samar da kayayyaki ba tare da tangarda ba, da karuwar bukatu ba tare da tsayawa ba, da saurin ci gaban sana'o'i masu alaka da fasahohin zamani da dai sauransu, duk sun nuna cewa tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da farfadowa.
Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci ya samarwa kamfanonin kasa da kasa sabbin damammaki. Yanzu haka, kasar Sin na rubanya kokarin raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da zurfafa sabunta masana’antu, ta yadda sana'o'i masu alaka da fasahohin zamani za su bunkasa cikin sauri.
A farkon rabin bana, saurin karuwar kudin da aka samu daga sana’ar kere-kere bisa fasahohin zamani, da kuma saurin karuwar jarin da aka zuba a sana’ar dukkansu sun karu matuka. Kana yawan hajojin zamani da ake samarwa ba tare da gurbata muhalli ba, kamar su mutum-mutumin inji masu ba da hidima, da motoci masu amfani da sabbin makamashi, ya karu fiye da kaso 10%. Ana raya masana’antu zuwa na zamani kuma ba tare da gurbata muhalli ba.
Har ila yau, darajar motoci, da jiragen ruwa, da kananan kayayyakin laturoni na “Integrated circuit” da sauransu, wadanda Sin ta sayar ga ketare sun karu matuka a farkon rabin shekarar ta bana, lamarin da ya kara azama kan kyautatuwar tsarin cinikayyar kasa da kasa na kasar Sin.
Yau Litinin ne shugabannin JKS suka fara zaman taro na 3 na kwamitin kolin jam’iyyar karo na 20, inda za a tsara ayyukan da ke shafar fannin kara zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, na zamanantar da kasar Sin.
Kasashen duniya na sa ran cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar wa duniya kyakkyawar makomar ci gaba, da kuma samar wa kamfanonin kasa da kasa sabbin damammaki. (Tasallah Yuan)