logo

HAUSA

Mambetova Elnura, ‘yar kasar Kyrgyzstan da ke amfana sosai a karkashin inuwar BRI

2024-07-15 16:07:17 CMG Hausa


Birnin Xi’an shi ne mafarin hanyar Siliki ta zamanin da. Wannan hanyar cinikayya da aka kafa sama da shekaru 2,000 da suka gabata, ta hada Sin da tsakiyar Asiya da Turai.

Xi’an ya ja hankalin jama’a daga kasashen dake kan hanyar Siliki domin karatu ko kasuwanci. 

Wadannan baki, wadanda suka samu gindinsu a birnin Xi’an, sun taimaka wajen kulla zumunta tsakanin Xi’an da kasashensu dake kan hanyar siliki, ta hanyar tattalin arziki da cinikayya da musayar al’adu.

Mambetova Elnura daga garin Issyk-Kul na kasar Kyrgyzstan dake tsakiyar Asiya, daya ce daga cikin baki wadanda suke daukar Xi’an a matsayin gidansu na biyu. Elnura, wadda aka sanyawa sunan Sinanci Ye Liya, ta fara zama a Xi’an tun daga shekarar 2015. A 2018, ita da mijinta, Chao Yonglin, dan asalin Xi’an, sun kafa wani kamfanin kasa da kasa na cinikayya ta yanar gizo, wanda ke tafiyar da harkokin cinikayya da musayar al’adu tsakanin kasa da kasa. 

Elnura na kaunar harshe da al’adun Sinawa tun tana ‘yar karama. Ta karanci harshen Sinaci a jami’ar kasar Kyrgyzstan da aka yi wa lakabi da sunan Jusup Balasagyn, tsakanin 2008 zuwa 2012. Bayan ta kammala a 2012, ta yi aiki a matsayin malamar Sinanci a jami’ar.

A shekarar 2015, ta koma Xi’an domin karatun digiri na biyu a fannin nazarin kasuwanci a jami’ar Chang’an. Elnura ta bayyana cewa, “Xi’an wanda a baya ake kira da Chang’an, ya yi nasarar hada tarihi da zamani. Tun da na zo birnin na kamu da sonsa. Abun da ya fi burge ni a Xi’an shi ne tsohuwar ganuwar dake tsakiyar birnin. Ganuwar na wakiltar dadadden tarihi da al’adun birnin masu zurfi, haka kuma ta shaida ci gaban da birnin ya samu.”

Har yanzu tana tuna karo na farko da ta ziyarci dakin adana kayayyakin tarihi na daular Tang, inda ta ga taswirar tsohuwar hanyar Siliki. Elnura ta ce, “hanyar ta ratsa ta kasata, da kuma garinmu. Na ga bayanan tarihi da suka nuna garin Suyab na kasar Kyrgyzstan, wanda a baya ake kira Ak-Beshim, muhimmin gari a kan tsohuwar Hanyar Siliki, kuma mahaifar Li Bai, fitaccen mawaki na Daular Tang, wadda ta kasance daga shekarar 618 zuwa 907 a tarihin kasar Sin. Ban da wannan kuma, akwai yiwuwar Xuan Zang, limamin addinin Buddha wanda ya rayu daga shekarar 602 zuwa ta 664, ya taba ziyartar garinmu. Ban taba tunanin Sin da Kyrgyzstan na da kusanci haka tun a zamanin baya ba.”

A watan Yunin 2016, jami’ar Chang’an ta shiryawa dalibai daga kasashen dake kan hanyar Siliki ziyara zuwa Yanliang, wanda ake kira da birnin sufurin jiragen sama na kasar Sin. A yayin ziyarar ne Elnura ta hadu da Chao Yonglin.

Elnura ta bayyana cewa, “ban taba tunanin zan auri dan wata kasa ba. Amma kuma idan ana batu na soyayya, ba a la’akari da inda mutum ya fito ko kadan. Mijina yana da karfin hali da hazaka, kuma yana kula da mu sosai.”

Elnura ta kara da cewa, “Na shiga, kuma na ci gajiyar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. A Xi’an, na samu farin cikin samun iyali da kuma ci gaban sana’ata.”

Yayin da shawarar ke samun ci gaba, kamfanin Elnura da mijinta na samun ci gaba a hankali. Su kan gudanar da kasuwancin da ya shafi shige da ficen kayayyaki da kamfanonin kasashen tsakiyar Asiya.

Elnura ta bayyana cewa, “Muna sayar da kayayyakin kasar Sin, kamar suturu da takalma da safa da kayan wasan yara da na laturoni da ababen hawa masu amfani da sabon makamashi da fulawa da naman sa da na rago. Kayayyakin kasar Sin masu inganci da araha, sun yi fice a kasata, kuma kayayyakin da ake samarwa a Kyrgyzstan su ma suna samun karbuwa sosai a kasuwar kasar Sin.”

A cewar Elnura, harkar kasuwnaci da suke yi ta intanet tsakanin kasa da kasa ya ci gajiya daga hidimar sufurin jirgin kasa na Chang’an na kasar Sin zuwa Turai, wanda ya fara aiki a Nuwamban 2013. 

Wata kididdiga da hukumar kula da ci gaban kasa da gyare-gyare ta fitar a watan Satumban 2023, ta bayyana cewa, jiragen kasa kirar Chang’an na kasar Sin zuwa Turai, dake tashi daga Xi’an ko zuwa Xi’an, sun bayar da gagarumar gudunmuwa ga gina muhimmiyar hanyar cinikayya tsakanin kasa da kasa, musamman bisa la’akari da matukar ingancinsu da araha. Cikin shekaru 10 da suka gabata, jiragen kasa na dakon kaya sun yi tafiye-tafiye 77,000 tsakanin Sin da Turai, inda suka tsaya a birane 217 na kasashen Turai 25.

A watan Fabrairun shekarar 2024, kamfanin jiragen sama na China Southern na kasar Sin ya kaddamar da sufurin jirgin sama kai tsaye tsakanin Xi’an da Bishkek, babban birnin Kyrgyzstan.

Elnura ta bayyana cewa, awoyi 4 kadai suke bukata na tafiya tsakanin biranen biyu. Ta yi ammana hanyar za ta bunkasa yawon bude ido a tsakiyar Asiya, kuma daga bisani za su zurfafa musaya tsakanin Sin da tsakiyar Asiya.

Elnura ta kara da cewa, “mun shirya tsara wani shirin kasuwanci na yawon bude ido tsakanin kasa da kasa a nan gaba. Na yi ammana, ta hanyar zurfafa shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da kuma hada hanyoyin sufurin jirgin sama daga Xi’an zuwa kasashe 5 na tsakiyar Asiya, Kyrgyzstan da tsakiyar Asiya za su samu karbuwa a matsayin wuraren yawon bude ido ga Sinawa.”

Yanzu Elnura tana karatun digirin digirgir a fannin nazarin harshen Sinanci, a jami’ar horar da malamai ta lardin Shaanxi dake birnin Xi’an. Nazarin da take yi na mayar da hankali ne kan yaduwar al’adun Sinawa a kasashen waje.

Elnura ta ce, “Kyrgystan daya ne daga cikin kasashe na farko da suka bayar da goyon baya tare da shiga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Shawarar ce ta sauya rayuwata da tabbatar da cikar burina na kasuwaci. Zan so in gina gadar musayar al’adu tsakanin jama’ar Sin da Kyrgyzstan tare da bayar da gudunmuwa ga abotar dake tsakanin mutanen kasashen biyu.”(Kande Gao)