logo

HAUSA

Sin ta bukaci WTO ta samar da majalisar kwararru masu shiga tsakani game da takaddama da Amurka game da EVs masu rangwame

2024-07-15 20:53:00 CMG Hausa

Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bukaci kungiyar cinikayya ta duniya WTO, da ta kafa wata majalisar kwararru da za ta shiga tsakani don gane da takaddamar ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi da aka samarwa rangwame, karkashin dokar IRA ta dakile hauhawar farashi da Amurka ta kaddamar.

A tsakiyar watan Agustan shekarar 2022 ne aka amince da dokar ta IRA, wadda ke da nufin kashe kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 369, a fannonin kare muhalli da samar da makamashi mai inganci. Har ila yau, tanajin ya kunshi samar wa motoci masu aiki da lantarki da aka kera a Amurka ta arewa, da kayayyakin hada batura na Amurka wani lamuni na haraji.

Game da hakan, a watan Maris da ya gabata, kasar Sin ta bukaci WTO ta shiga tsakani, domin warware takaddama da Amurka game da wasu bangarori na lamunin haraji karkashin dokar IRA, da nufin ingiza samar da ababen hawa masu aiki da lantarki, da ayyukan da suka shafi sabbin makamashi, to sai dai kuma Amurka ta ki amincewa a kai ga matsaya.   (Saminu Alhassa)