logo

HAUSA

Jihar Gombe tana fatan za a ci gaba da aikin hakar danyen mai a jihar

2024-07-15 09:22:43 CMG Hausa

Gwamnan jihar Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya Alhaji Inuwa Yahaya ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya taimaka wajen sanya baki domin tabbatar da ganin an ci gaba da aikin hakar danyen mai a yankin Kolmani dake jihar.

Gwamnan ya bukaci hakan ne a karshen makon jiya lokacin da ya gana da shugaban a fadarsa dake birnin Abuja, ya ce tun lokacin da gwamnatin da ta shude ta kaddamar da fara aikin a cikin watan Nuwamban 2022 bayan gano man a kan iyakar jihar da Bauchi, babu wani abu na ci gaba da aka sake samu daga aikin.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A lokacin da yake zantawa da manema labarai dake fadar shugaban kasa, gwamnan na jihar ta Gombe wanda ya bayyana damuwa bisa yadda aikin ke yin tafiyar hawainiya, ya ce, hakika jinkirin ci gaba da aikin gadan-gadan babbar asara ce ga jihohin dake arewacin Najeriya.

Ya ce, kamfanin man kasar NNPC tare da abokan huldarsa da aka dorawa alhakin gudanar da aikin, sun yi watsi da aikin tun bayan lokacin da aka kaddamar da shi shekaru biyu da suka shude.

Ko da yake gwamnan ya ce, yana fatan ganawarsa da shugaban zai sanya a dawo da ci gaba da aikin ka-in da na’in.

“Duk aikin dake da nasaba da man fetur da iskar gas hurumi ne da ya shafi gwamnatin tarayya, babu abun da za mu iya yi, kamfanin main a NNPC shi kadai yake da cikakken damar aiwatar da duk wasu harkokin da suka shafi fetur da gas a fadin tarayyar kasa.” (Garba Abdullahi Bagwai)