Sojojin Sudan sun kashe sama da dakarun sa kai 100 a Khartoum
2024-07-15 09:49:03 CMG Hausa
Rundunar sojin Sudan ko SAF ta sanar a ranar Lahadi cewa, sama da dakarun sa kai na gaggawa ko RSF 100 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a wani harin da ta kai a birnin Khartoum a ranar Asabar.
A cikin sanarwar da SAF din ta fitar ta ce, a ranar Asabar sojojinta sun gudanar da ayyuka masu inganci a babban birnin kasar, inda aka lalata motocin yakin RSF da dama.
Tun tsakiyar watan Afrilun shekarar 2023 ne Sudan ta fada cikin kazamin rikici tsakanin SAF da RSF, wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan mutane a kalla 16,650, a cewar wani sabon rahoto daga ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD a watan jiya.
Kazalika, sama da mutane miliyan 7.7 ne suka rasa matsugunansu a kasar Sudan tun bayan barkewar rikicin, yayin da wasu kimanin miliyan 2.2 suka tsallaka kan iyakokin kasashen makwabta, a cewar alkaluman da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta fitar a ranar 25 ga watan Yuni. (Yahaya)