Hukumar FBI ta sanar da wanda ake zargi da harbin Trump
2024-07-15 10:25:11 CMG Hausa
Jim kadan bayan tsira daga yunkurin kashe shi da aka yi, tsohon shugaban Amurka Donald Trump, wanda ake tsammanin shi zai yi wa jam’iyyar Republican takarar shugabancin kasar, ya bukaci Amurkawa su zama tsintsiya madaurinki daya, kuma kada su bari mugunta ta yi nasara. An yi yunkurin kashe Trump ne yayin wani gangami a Butler na jihar Pennsylvania.
Hukumar tsaro ta FBI na binciken lamarin a matsayin yunkurin kisa, inda ta bayyana Thomas Mathew Crooks mai shekara 20, a matsayin wanda ake zargi.
Bindigar da aka samu a wurin da lamarin ya auku, ya nuna cewa mahaifin Mathew Crooks ya sayi bindigar bisa doka. An kuma samu ababen fashewa a cikin motar wanda ake zargin.
Cikin wani gajeren tsokaci a daren ranar Asabar, shugaban kasar Joe Biden ya bayyana lamarin a matsayin hauka, yana mai cewa abu ne da ba za a lamunta ba.
Yayin da wani dan jarida ya nemi jin ra’ayinsa game da lamarin, Biden ya amsa da cewa, “Ina son tabbatar da mun samu dukkan hujjoji kafin in tsokaci.” (Fa’iza Mustapha)