logo

HAUSA

Beijing: An bude taron karawa juna sani game da bunkasa ilimin kimiyya a matakin farko

2024-07-14 21:41:55 CMG Hausa

 

A yau Lahadi ne aka bude taron karawa juna sani na kasa da kasa game da bunkasa ilimin kimiyya a matakin farko ko ICBS, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Taron na ICBS ya hallara masana kimiyya da kuma malamai sama da 800 daga gida da kasashen waje.

Cikin makwanni 2 dake tafe, za a gabatar da makalu na ilimi da kuma wasu taruka daban daban sama da 500, da nufin yin musayar nasarorin zamani a fannonin raya kimiyya a matakin farko, da hangen nesa a fannin ci gaban ginshikan bangarorin bincike.

Kaza lika, wasu 4 da suka samu lambar yabon Fields da wasu 3 da suka samu lambar yabon Turing, da wanda ya samu lambar yabon Nobel da kuma ‘yan kwalejin nazarin kimiyya sama da 70 daga kasashe daban daban za su halarci taron.    (Saminu Alhassan)