logo

HAUSA

Nijar: An cafke da dama daga fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Koutoukale

2024-07-14 21:21:28 CMG Hausa

 

Wata sanarwar da rundunar sojojin Nijar ta fitar a jiya Asabar, ta ce jami’an tsaro sun yi nasarar cafke da yawa daga fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Koutoukale mai matukar tsaro dake da nisan kilomita kusan 50 daga arewa maso yammacin birnin Yamai, fadar mulkin kasar.

Rundunar sojin ta Nijar ta ce, wani hargitsi da ya auku ne ya baiwa gwamman fursunonin damar tserewa a ranar Alhamis, sai dai kuma sojoji, da dakarun rundunar FDS sun bazama domin sake kamo wadanda suka tsere, kuma da taimakon sassan jami’an tsaro daban daban, sun yi nasarar cafke da dama daga cikinsu. Kaza lika, an yi wa yankin da lamarin ya faru kawanya, yayin da ake shirin fara shawagi ta sama domin gano sauran wadanda suka tsere.

A daya hannun kuma, majiyar rundunar sojin kasar ta ce, dakarun FDS masu aiki a yankin Gorou, yankin da fursunonin suka tsere sun yi nasarar ganowa, da kuma hallaka wasu ‘yan ta’adda su uku da suka tsere daga gidan yarin na Koutoukale.    (Saminu Alhassan)