Trump zai halarci babban taron jam’iyyar Republican a makon gobe duk da raunin harbin bindiga da aka yi masa
2024-07-14 16:08:22 CMG Hausa
Duk da raunin da ya samu yayin da wani dan bindiga ya harbe shi a birnin Butler na jihar Pennsylvania a jiya Asabar, lokacin da yake yi wa magoya bayansa jawabi, tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump zai halarci babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyarsa ta Republican, wanda zai gudana a mako mai zuwa kamar yadda aka tsara.
An dai tsara gudanar da taron jam’iyyar ta Republican ne a birnin Milwaukee na jihar Wisconsin, tun daga gobe Litinin zuwa ranar Alhamis 18 ga watan nan, inda ake sa ran bayyana sunan Trump a matsayin wanda zai yi wa jam’iyyarsa takara, a babban zaben kasar na ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Wani faifan bidiyo na nuna yadda wasu magoya bayan Trump dake wurin da harbin ya auku na ihu, yayin da aka hango jini na zuba ta gefen kai da kunnen mista Trump.
Shafin sada zumunta na X, na hukumar jami’an tsaron farin kaya ta Amurka ya bayyana cewa, wani dan bindiga ya yi harbi sama da sau daya zuwa wurin da Trump yake, daga saman wani bene a wajen dandalin taron. Nan da nan kuma jami’an tsaro suka harbe dan bindigar. Jami’an sun kuma ce, Trump ba ya cikin hadari, sai dai kuma sakamakon harin da dan bindigar ya yi, ya hallaka wani mai halartar gangamin guda, tare da jikkata wasu mutane 2 wadanda ke cikin yanayi mai tsanani.
Tuni dai shugaban Amurka Joe Biden ya yi Allah wadai da harin na jiya Asabar. (Saminu Alhassan)