logo

HAUSA

Cinikin waje na kasar Sin ya samu sakamako mai kyau a rabin farko na shekarar bana

2024-07-13 17:17:13 CMG Hausa

Kasar Sin ta fitar da rahoto game da yadda aka gudanar da ciniki tsakaninta da kasashen waje a rabin farkon shekarar da muke ciki, wanda ya nuna sakamako mai matukar kyau da aka samu a bangaren.

Bisa rahoton wanda aka fitar jiya Jumma’a, jimillar darajar kayayyakin da aka shigo da su kasar da wadanda aka fitar zuwa kasashen waje, ta kai kudin Sin Yuan tiriliyan 21.17, wadda ta karu da kashi 6.1% idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, wanda ya samu ci gaba tare da kara karfafa na baya.

A cewar kafofin yada labarai na kasashen waje, ciki har da jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya, ba abu ne mai sauki cinikin waje na kasar Sin ya cimma irin wannan sakamako wanda ya wuce hasashen da aka yi ba, bisa la’akari da yadda kasashen yammacin duniya ke fafutukar "katse mu’amala" da kasar, da yadda kasar Amurka da kasashen Turai ke sanya mata haraji, lamarin da ya dauki hakalin jama’a a fannin tattalin arzikin kasar ta Sin.

Alkaluman sun nuna cewa, a rabin farko na bana, cinikin kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen waje ya karu da 5.2 % idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, hakan ya nuna cewa, yawan kayayyakin da ake shigowa da su kasar yana karuwa akai-akai.

La’akari da yadda gwamnatin kasar Sin ke kaddamar da wasu manufofi masu kyau na bude kofa ga waje, za’a kara samar da sauki ga shigowar hajojin kasashe daban-daban cikin kasuwannin kasar Sin, kana kamfanonin jarin waje za su kara samun damammaki wajen raya harkokinsu a kasar Sin. (Bilkisu Xin)