Zakarun gasar Olympics 42 za su jagoranci tawagar kasar Sin a gasar Olympics ta Paris
2024-07-13 17:48:36 CMG Hausa
Kasar Sin za ta tura tawagar da ta kunshi ‘yan wasa 405, ciki har da zakarun gasar Olympics 42, zuwa gasar wasannin Olympics na Paris dake karatowa.
Sanarwar da aka yi a hukumance a yau Asabar, ta ce tawagar ta kunshi ‘yan wasa maza 136 da mata 269, wadanda za su fafata a wasannin 30, yayin gasar da za a kaddamar ranar 26 ga wata.
Matsakaicin shekarun ‘yan wasan shi ne 25, kuma wannan shi ne karo na farko da ‘yan wasa 223 daga cikinsu za su halarci gasar wasannin Olympics.
Sama da ‘yan wasa 10,000, daga kasashe da yankuna sama da 200 ne ake sa ran za su fafata a gasar Olympics da za ta gudana a birnin Paris na Faransa daga ranar 26 ga watan nan, zuwa 11 ga watan Augusta. (Fa’iza Mustapha)