logo

HAUSA

Hira da shugaban Guinea-Bissau Umaro Mokhtar Sissoco Embalo

2024-07-13 21:09:10 CMG Hausa

Da yammacin ranar 10 ga watan Yuli, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Guinea-Bissau Umaro Mokhtar Sissoco Embalo, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin. A yayin tattaunawar, shugabannin kasashen biyu sun amince da inganta huldar dake tsakanin Sin da Guinea-Bissau, zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare. Shugaba Embalo ya bayyana a wata hira da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, inganta wannan alaka na da matukar muhimmanci.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a duniya. A cewarsa, "A ko da yaushe kasar Sin tana goyon bayan matsayin kasar Guinea-Bissau a MDD, a duk lokacin da muke bukatar goyon bayan kasar Sin, Sin tana goyon bayanmu ba tare da wata tangarda ba. Muna kuma goyon bayan kasar Sin har kullum."

Yayin da yake magana kan tasirin hadin kai tsakanin Sin da Afirka ga kasashe masu tasowa da ma duniya baki daya, Embalo ya ce, a cikin kasashen Afirka 54, babu wadda ba ta samu nasara sakamakon kokarin kasar Sin ba. Har ila yau, ya ce Sin ce kasar da ta fi yawan ofisoshin jakadanci a Afirka, hakan ya nuna muhimmancin da take baiwa nahiyar. (Bilkisu Xin)