logo

HAUSA

Fahimtar manufar kasar Sin ta yin kwaskwarima a sabon zamani ——Da zarar an mallaki hanyar da ta dace, za a iya samun sakamako sau biyu bisa ga rabin kokari

2024-07-13 16:43:32 CMG Hausa

A ranar 23 ga watan Mayun shekarar 2024, an gudanar da taron karawa juna sani tsakanin kamfanoni da masana kan yin kwaskwarima a birnin Jinan, babban birnin lardin Shandong dake gabashin kasar Sin, wanda shugaban kasar Xi Jinping ya jagoranta, inda ya bayyana cewa, “A yayin da ake yin kwaskwarima, ba kawai ana bukatar kawar da tsofaffin sassan da ba su dace ba, har ma da kafa sababbin tsare-tsaren da suka dace, da zarar an mallaki hanyar da ta dace, za a iya samun sakamako sau biyu bisa ga rabin kokari.”

Wadanne dabaru aka yi amfani da su wajen yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin ta yi a cikin shekaru 40 da suka gabata?

“Bari wasu su sami arziki tukuna” shi ne ainihin ra'ayin marigayi Deng Xiaoping wajen jagorantar yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. An tsara wannan manufar ne bisa ga rashin daidaiton ci gaban al’umma a kasar Sin a wancan lokaci, kuma ta sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar baki daya. Amma, “wadatar gama gari” shi ne babban burin aiwatar da wannan manufar.

Domin cimma wannan buri, Xi Jinping ya shirya wani “wasan dara”. Tabbatar da dunkulewa da hadin kai hanya ce mai muhimmanci a gare shi don buga wannan wasan na dara da kyau, kuma ya kasance muhimmin bangare na hanyoyinsa na yin kwaskwarima.

“A halin yanzu, mun kai wani sabon matsayi na tarihi na yin kwaskwarima, kuma mun gamu da sabbin matsaloli masu yawa da ba a taba ganin irinsu ba. Dole ne mu nuna karfin zuciya da hikimar siyasa, da kuma mai da hankali kan kafa tsare-tsare, da tabbatar da dunkulewa da ma hadin kai a yayin da ake yin kwaskwarima, hakan za a karfafa ingantattun ayyuka a fannin.”

Wannan dabara ta yi fice musamman wajen yin gyare-gyare kan rashin daidaiton ci gaba a tsakanin yankuna daban daban a kasar Sin. A ganin Xi Jinping, rashin daidaituwa ya kasance a ko'ina, kuma dole ne a inganta samun daidaituwa a yayin da ake neman ci gaba. Wannan ita ce dabarar gano gaskiya ta samun daidaiton ci gaba a tsakanin yankuna daban daban. (Bilkisu Xin)