logo

HAUSA

MDD ta yi hasashen yawan al’ummar duniya zai kai matsayin koli a wannan karnin

2024-07-12 13:57:28 CMG Hausa

MDD ta fitar da wani rahoto mai lakabin “Hasashen Yawan Al’ummar Duniya na 2024: Takaitaccen Sakamako” wanda ya nuna cewa, ana sa ran yawan al’umma zai kai matsayin koli a tsakiyar shekarun 2080, inda cikin shekaru 60 masu zuwa adadin zai karu daga biliyan 8.2 a 2024 zuwa kusan biliyan 10.3 a tsakiyar shekarun 2080, sannan kuma zai ragu zuwa kimanin biliyan 10.2 a karshen karnin. (Fa’iza Mustapha)