Ministan harkokin wajen kasar Sin ya soki kungiyar NATO, yana mai kira da a gudanar da ciniki mara shinge
2024-07-12 14:02:12 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya yi kira ga Netherlands da ta mara baya ga gudanar da cinikayya ba tare da shinge ba, da kuma kare karkon tsarin ayyukan masana’antu da na samar da kayayyaki.
Wang Yi ya bayyana haka ne yayin tattaunwarsa da sabon takwaransa na Netherlands, Caspar Veldkamp ta wayar tarho a jiya Alhamis.
Ya kuma musanta tsokacin da kungiyar tsaro ta NATO ta yi kwanan nan yayin taronta a Washington. Yana mai cewa, bai kamata bambancin tsarin siyasa da ra’ayi tsakanin Sin da NATO ya zama dalilin da kungiyar za ta ingiza fito na fito da Sin ba.
A cewarsa, kasar Sin ba za ta lamunci zarge-zarge mara tushe ba. Yana mai bayyana Sin a matsayin babbar kasar da mafi kyaun tarihi na zaman lafiya da tsaro, kuma ta kasance mai ingiza zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
A nasa bangare, Caspar Veldkamp, ya ce dangantakar Netherlands da Sin na da karfi da juriya. Kuma yayin da ake fuskantar birkecewar yanayin duniya, Netherlands ba ta goyon bayan raba gari da kasar Sin, kuma a shirye take ta ci gaba da tuntubar Sin domin inganta dantankarsu a zahirance. (Fa’iza Mustapha)