An sake dage taro tsakanin kungiyar kodago da shugaba Tinubu bayan gaza samun matsaya
2024-07-12 09:23:51 CMG Hausa
Ba a samu cimma matsaya ba a taron da shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gudanar jiya Alhamis tare da shugabannin kungiyar kodagon kasar ba.
Taron wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, an dage shi zuwa makon gobe, inda za a ci gaba da tattaunawa kan batun mafi kankantar albashi na kasa.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, shugaban kungiyar Kodago na kasar Mr Joe Ajaero ya ce, ba su samu daidaitawa da gwamnati a zaman nasu ba, amma dai ya tabbatar da cewa, za su koma domin zama da mambobin su domin yi musu bayanin sakamakon abun da suka tattauna da shugaban kasa.
Ya kara da cewa, har yanzu suna kan burinsu na neman sai gwamnati ta amince da Naira dubu 250 a matsayin mafi kankantar albashi.
A nasa bangaren ministan yada labarai na kasar Alhaji Muhammed Idris ya ce, ganawar da shugaban kasa ya yi da jagororin kungiyoyin kodagon kasar ci gaba ne daga jerin tuntuba da yake yi da masu ruwa da tsaki domin samar da matsayar bai daya kan batun sabon tsarin albashi na kasa.
“Kungiyar kodago da gwamnati za su kai ga cimma yarjejeniya, amma yanzu a dage ci gaba da zamansu zuwa mako guda, bayan da kungiyar kodagon ta nuna bukatar a ba ta sati daya domin dai ta tuntubi sauran mambobinta, kuma muna da kyakkyawan fatan cewa a karshe dai za a samar da matsaya ta karshe da za ta sanya kowane dan Najeriya farin ciki.” (Garba Abdullahi Bagwai)