Darajar cinikayya tsakanin Sin da ketare ta kai wani sabon mataki a rabin farko na bana
2024-07-12 14:58:38 CMG Hausa
Darajar cinikayya tsakanin Sin da kasashen ketare ta kai wani sabon mataki a rabin farko na bana, lamarin da ya samar da karin kuzari ga farfadowar tattalin arzikin kasar.
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce tsakanin Junairu zuwa Yuni, yawan kayayyakin da aka yi cinikayyarsu ya karu da kaso 6.1% a kan na bara, inda ya kai yuan triliyan 21.17, kwatankwacin dala triliyan 2.97. Kayayyakin da kasar Sin ta ke fitarwa ketare kuma ya karu da kaso 6.9 yayin da wadanda ke shigowa kasar ya karu da kaso 5.2