Sin da Rasha sun gudanar da atisaye tare
2024-07-12 20:03:47 CMG Hausa
A yau Juma’a ne kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Zhang Xiaogang ya bayyana cewa, rundunar sojin Sin da na Rasha sun fara atisayen hadin gwiwa a ruwa da sararin samaniya kusa da birnin Zhanjiang dake kudancin kasar Sin a farkon watan Yulin nan.
Kakakin a taron manema labarai ya bayyana cewa, “Atisayen hadin gwiwa na teku na 2024” ana gudanar da shi ne bisa tsarin ayyukan soja na shekara-shekara na kasar Sin da Rasha da yarjejeniyoyin kasashen biyu, kuma za a gudanar da shi har zuwa tsakiyar watan Yuli.
Ana gudanar da atisayen ne da nufin nuna kuduri da karfin sojojin wajen magance barazanar tsaron teku tare da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da yankin, a cewarsa.
Sai kuma a cewar rahoto daga kafafen yada labarai, hotunan tauraron dan Adam na kasuwanci sun nuna cewa a baya-bayan nan babban jirgin ruwa mai saukar jiragen sama na kasar Sin mai suna Shandong ya bayyana a ruwan teku dake kusa da kasar Philippines, da yake mayar da martani, mai magana da yawun ma'aikatar Zhang Xiaogang, ya ce Shandong ya je ruwan tekun ne don gudanar da horon yakin teku mai nisa, wanda kuma tsari ne na yau da kullum na shekara-shekara, kuma ya dace da dokokin kasa da kasa. (Yahaya)