Kasar Sin ta yi kakkausar suka kan kalaman tsokana da sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO ya yi kan kasar
2024-07-12 20:51:32 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya ce, kasarsa ta yi Allah-wadai da kalaman karya da tsokana da sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO ya yi kan kasar.
Jami’in ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa a yau Jumma’a.
Jiya Alhamis ranar 11 ga wata, sakatare Janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya sake yin tsokaci kan "barazanar Sin" a gun taron manema labarai na rufe taron koli na kungiyar.
Game da haka, Lin Jian ya kara da cewa, kalaman nasa na cike da tunani na yakin cacar baka da nuna bambancin ra’ayi, da kuma jirkita gaskiya. Duk nau'in wasan kwaikwayo mara kyau da ya yi, zai tada hankalin duniya, wanda kuma ya shaida cewa, a matsayinta na ragowar yakin cacar baka, da rura wutar adawa da kuma kafa kananan kungiyoyin siyasa, kungiyar NATO za ta kawo hadari da kalubale ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya.
Kaza lika, a yayin da yake ba da amsa kan kalaman da shugabannin kasashen Japan da Koriya ta Kudu suka yi a baya-bayan nan na cewa, wai tsaron arewacin tekun Atlantika ba ya rabuwa da tsaron arewa maso gabashin Asiya, Lin Jian ya bayyana fatansa na ganin kasashen yankin sun tsaya kan ingantacciyar hanyar hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya da tekun Pasifik, kada su yi aiki a matsayin "masu tsaro" na kungiyar NATO wajen habaka ayyukanta a yankin Asiya da tekun Pacific. (Bilkisu Xin)