Sarkin Lesotho ya bayyana niyyar nacewa ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya
2024-07-12 14:00:32 CMG Hausa
Sarkin Lesotho Letsie III ya bayyana a jiya Alhamis cewa, Lesotho tana daukar huldarta da kasar Sin da matukar muhimmanci, kuma za ta ci gaba da nacewa ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da ma zurfafa hadin gwiwarsu daga dukkan fannoni, da ingiza bunkasuwar huldar kasashen biyu zuwa gaba.
Letsie III ya fadi haka ne yayin da ya karbi takardar nadin sabon jakadan Sin a kasar, Yang Xiaokun a wannan rana, a Masero fadar mulkin kasar. (Amina Xu)