logo

HAUSA

Fursunoni sun tsere daga gidan yari mai dauke da ‘yan ta’adda a Nijer

2024-07-12 10:31:31 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta Jamhuriyar Niger ta ce wasu fursunoni sun tsere daga wani gidan yari mai dauke da ’yan ta’adda, dake  yankin Tillabery na yammacin kasar.

Sai dai cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar ba ta bayyana yadda fursunonin suka tsere ko adadinsu ba.

Wannan gidan dai na dauke da mambobin kungiyar BH da na wasu kungiyoyi masu dauke da makamai na yankin Sahel. (Fa’iza Mustapha)