logo

HAUSA

Ibrahim Traore ya jadadda niyyarsa ta mulkin kasar a tsawon shekaru biyar masu zuwa

2024-07-12 09:45:11 CMG Hausa

A ranar jiya Alhamis 11 ga watan Yulin shekarar 2024 a birnin Ouagadougou, kaftin Ibrahim Traore ya gabatar da hangensa na shekaru biyar masu zuwa na kasancewa kan karagar mulkin Burkina Faso, a filin wasannin motsa jiki na birnin Ouagadougou da ya cika makil da mutane.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

A gaban ’yan kasa da suka zo, kaftin Ibrahim Traore ya tabbatar da matakin da ya dauka a watan Mayun da ya gabata a yayin zaman taron kasa game da karin wa’adin mulkin rikon kwarya da shekaru biyar nan gaba.

A cikin jawabinsa na manufofin siyasa na fiye da awa guda, kaftin Ibrahin Traore ya tabo batutuwa da dama da suka shafi ci gaban kasa, inda ya fara da batun tsaro, inda ya ce, babu wata tattaunawa tare da ’yan ta’adda, tare da wadannan mutane masu aikata manyan laifuka. Ko mu yake su ko su yake mu, mun zabi da mu yake su, daga nan ne za mu samun ’yancin kan mu.

A cikin jawabinsa, ya jaddada zargi kan kasashen yammacin duniya da a cewarsa suna son kawo fitina a yankin Sahel, tare da tabbatar da cewa suna da shaidun kasancewar sansanin sojoji Faransa a Benin da Cote d’Ivoire domin horar da ’yan ta’adda.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.