logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu girbi mai armashi a lokacin zafi na bana

2024-07-12 14:59:50 CMG Hausa

Alkaluma a hukumance sun nuna cewa, kasar Sin ta kara samun girbin hatsi mai armashi a lokacin zafi na bana.

Alkaluma daga hukumar kididdiga ta kasar Sin sun nuna cewa, jimillar hatsin da kasar ta samar a lokacin zafi na bana, ya kai ton miliyan 149.78, wanda ya karu da kaso 2.5 ko kusan ton miliyan 3.63 kan na shekarar da ta gabata. (Fa’iza Mustapha)