logo

HAUSA

Wasu mahara sun hallaka mutane 10 a jihar Benue ta shiyyar tsakiyar Najeriya

2024-07-11 09:45:19 CMG Hausa

Rahotanni daga jihar Benue ta shiyyar tsakiyar Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai, sun hallaka a kalla mutane 10 tare da kone gidaje a kauyen Olegumachi na karamar hukumar Agatu.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, shugaban karamar hukumar ta Agatu Phillip Ebenyakwu, ya ce maharan sun kutsa kai kauyen Olegumachi ne da daren ranar Talata, inda suka rika harbin mutane da bindigogi, suna wawashe kayayyakin abinci da kore dabbobi, tare da cinnawa a kalla gidaje 7 wuta.

Shugaban karamar hukumar ya ce sun sanar da ‘yan sanda aukuwar lamari da safiyar jiya Laraba.  (Saminu Alhassan)