logo

HAUSA

Ghana: Alkaluman hauhawar farashi sun ragu zuwa kaso 22.8 bisa dari a watan Yuni

2024-07-11 10:07:03 CMG Hausa

Hukumar kididdiga ta kasar Ghana GSS, ta ce alkaluman hauhawar farashin kayayyaki sun ragu zuwa kaso 22.8 bisa dari a watan Yunin da ya gabata, sabanin kaso 23.1 bisa dari da kasar ta samu a watan Mayu.

Babban jami’in kididdiga na hukumar ta GSS Samuel Kobina Annim, ya ce raguwar ta faru ne sakamakon faduwar farashin kayayyakin da ba na abinci ba a watan na Yuni. Kaza lika a cewarsa, in an kwatanta da watan Mayu, a watan na Yuni farashin kayayyakin da ba na abinci ba ya ragu da maki 2 zuwa kaso 21.6 bisa dari, yayin da farashin kayayyakin abinci suka karu da maki 1.4 wato zuwa kaso 24 bisa dari a watan na Yuni.

Har ila yau, mista Annim ya ce karuwar farashin kayayyakin da ake sarrafawa a cikin kasar, da na wadanda ake shigarwa daga ketare sun kai kaso 25 da 17.5 bisa dari a watan.

Kasar Ghana dake yankin yammacin Afirka na da albarkatun zinari, da cocoa, da danyen mai da take fitarwa kasuwannin duniya, kuma a halin da ake ciki tana aiwatar da kwaskwarima ga tattalin arziki ta amfani da lamunin dalar Amurka biliyan 3 da ta karba daga asusun IMF da nufin farfado da tattalin arzikin. Ana kuma sa ran sauye sauyen da kasar ke yi za su shawo kan kalubalen hauhawar farashin kayayyaki, da na musayar kudaden waje, da mummunan tasirin bashi dake addabar kasar a ‘yan shekarun baya bayan nan.   (Saminu Alhassan)