logo

HAUSA

Harkokin yawon shakatawa na fadada cikin sauri a Sin tun bayan fara hutun lokacin zafi

2024-07-11 08:10:07 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, a halin yanzu, ana samun karuwar masu yawon bude ido na kasa da kasa a kasar Sin, sakamakon manufar samar da iznin shiga kasar Sin ba tare da Visa ba da Sin ta fitar a kwanan baya. Haka kuma, harkokin yawon shakatawa a sassan kasar Sin suna karuwa cikin sauri bayan fara gudanar da hutun lokacin zafi a kasar.