logo

HAUSA

Shugaban CNSP Abdourahamane Tiani ya gana da shugabannin al’umomi da masu fadi a ji na Kawar

2024-07-11 09:56:22 CMG Hausa

Shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP kuma shugaban kasar Nijar birgadiye janar Abdourahamane Tiani ya yi wata ganawa a ranar jiya Laraba 10 ga watan Julin shekarar 2024 a fadar shugaban kasa dake birnin Yamai tare da masu fadi a ji da masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umomi na yankunan Kawar, arewacin N’gourti da arewacin Tesker domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan Agadez da Diffa.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ita dai wannan ganawa ta keke da keke, ta ja ragama ne kan matsalar tsaro da kuma bullo da hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da tsaro tare da shugaban kasa Abdourahamane Tiani.

A yayin wannan tattaunawa da ta gudana a gaban faraminista Ali Mahamane Lamine Zeine, da ministan cikin gida Mohamed Toumba, da ministan tsaron kasa Salifou Mody da kuma sauran manyan jami’an gwamnati da mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP. Shugaban kasa Abdourahamane Tiani ya bayyana fatan ganin wadannan wakilan al’umma na wadannan yankuna uku sun taka muhimmiyyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, da kuma hada kan ’yan Nijar wajen gina kasa da kare kasa daga abokan gaba da masu neman ta da zaune tsaye. Haka kuma shugaban kasa ya nuna cewa ya zama wajibi da hada karfi da karfe wajen kawo kwanciyar hankali da zaman jituwa, da kawar da duk wata hanyar daukar makamai domin neman ’yanci, wannan wani babban laifi ne da cin amanar kasa, kuma shugabannin kasa za su dauki dukkan matakan da suka dace domin kare ’yan Nijar baki daya da kare fadin kasa.

A nasu bangare wadannan wakilan al’umomin yankunan Kawar, N’Gourti da Tesker sun dauki alkawuran kawo gudunmuwarsu domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare kuma da ba da hadin kai ga hukumomin kasa wajen yaki da ’yan ta’adda, masu fadi da makami da kuma masu ikirarin tawaye a duk inda suka shiga.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.