logo

HAUSA

Kwadebuwa na aiwatar da matakan karfafa shari'a domin yaki da ta'addanci

2024-07-11 11:32:50 CMG Hausa

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Kwadebuwa Amadou Coulibaly, ya ce gwamnati na daukar karin matakai na karfafa matakan shari'a domin yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.

Amadou Coulibaly, wanda ya bayyana hakan jiya Laraba bayan kammala taron majalissar ministocin kasar, ya ce an samar da sashen musamman a kotun birnin Abidjan, don hukunta shari'u da suka shafi yaki da ta'addanci, ciki har da hukunta laifuka masu alaka ta kai tsaye da ta’addanci, da sauran manyan laifuka.

Jami'in ya kara da cewa "Matakan sun kunshi samar da horo a fannin bincike da gabatar da kararraki, da horaswa a bangaren gudanar da shari’a da zaman kotuna, da karfafawa, da tsara matakai daban daban domin kandagarkin aukuwar laifuka gwargwadon iko, da na gano maboyar ‘yan ta’adda, da sauran laifuka masu nasaba a dukkanin sassan yankunan kasar”. (Saminu Alhassan)