logo

HAUSA

Kungiyar tsaro ta NATO ba za ta iya dora alhakin rikicin Ukraine kan kasar Sin ba

2024-07-11 21:30:45 CMG Hausa

Jiya Laraba 11 ga wata, taron koli na kungiyar tsaro ta NATO ya bayar da wata sanarwa, wadda ta kaddamar da mummunan suka kan kasar Sin bisa yadda kungiyar ke yin hadin gwiwa da dabarun Amurka na hana ci gaban kasar Sin, inda ta yi karya na cewa Sin ce ke rura wutar rikicin Rasha da Ukraine, wadda ke haifar da kalubale mai tsauri ga tsaron tekun Atlantika.

Yau kusan shekaru biyu da rabi ana gwabza rikici tsakanin Rasha da Ukraine. Mutane da dama sun fahimci cewa, bayan kawo karshen yakin cacar baka, kungiyar tsaro ta NATO ta ci gaba da kara kaimi wajen fadada ayyukanta na gabas karkashin jagorancin kasar Amurka, inda a kullum take danne sararin tsaron kasar Rasha, wanda shi ne asalin tayar da rikicin Rasha da Ukraine.

Domin kaucewa daukar alhakinta a rikicin Rasha da Ukraine, NATO ta gabatar da wani “karkataccen ra'ayi”, wato neman shafa wa kasar Sin kashin kaji ta hanyar kirkira labaran karya. Amma, hakan ba zai iya boye alhakin dake kan NATO ba.

Kamar yadda aka sani, kasar Sin ba ita ce mai tayar da rikicin Ukraine ba, kuma ba ta cikin rikicin. Babban matsayin kasar Sin game da batun Ukraine, shi ne inganta yin shawarwari cikin lumana da warware rikicin a siyasance, kuma kasar ba ta taba samar da muggan makamai ga kowane bangare dake cikin rikicin ba, kana tana mayar da hankali sosai kan fitar da kayayyakin da ake amfani da su a fannonin aikin soja da na jama’a.

A matsayinta na wanda ya kaddamar da wannan rikicin, ya kamata Amurka da NATO da ke karkashin jagorancinta su daina dora laifin kan kasar Sin, kuma su dauki kwararan matakai don inganta sassaucin halin da ake ciki.

Kamar yadda kasar Sin ta ce, sai in dukkan manyan kasashen duniya sun taka muhimmiyar rawa maimakon kawo cikas, za a kai ga matakin tsagaita bude wuta da sauri a tsakanin Rasha da Ukraine. (Bilkisu Xin)