logo

HAUSA

An hallaka kwamandan 'yan a ware a yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru

2024-07-11 09:34:27 CMG Hausa

Rundunar sojin kasar Kamaru ta ce ta yi nasarar hallaka wani kwamandan dakarun ‘yan a ware da ake yiwa lakabi da "Commander Iron", tare da wani mayaki dake tare da shi, lokacin da sojoji suka kai sumame maboyarsa dake unguwar Mancho, a birnin Bamenda na yankin arewa maso yammacin kasar inda ake magana da turanci.

Majiyar sojojin kasar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, cewa an kaddamar da farmakin a maboyar jagoran 'yan a waren ne da sanyin safiyar jiya laraba, an kuma yi nasarar hallaka dakarun su 2 cikin nasara.

Har ila yau, majiyar ta ce a baya bayan nan ne "Commander Iron" ya maye gurbin tsohon kwamandan 'yan a waren da shi ma sojoji suka hallaka, yayin wani farmaki da suka kai masa cikin makon jiya. (Saminu Alhassan)