logo

HAUSA

Gwamnatin sojan Mali ta dawo da ayyukan jam’iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hulla da aka dakatar a watan Afrilun shekarar 2024

2024-07-11 10:10:13 CMG Hausa

A cikin wata sanarwa ta gidan rediyo da talabijin na kasar Mali, sojojin dake mulki sun sanar a ranar jiya Laraba 10 ga watan Julin shekarar 2024 da ba da umurnin dawo da ayyukan jam’iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hula. Ayyukan da aka dakatar a ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2024, tare da janyo suka daga kasashen yammacin duniya.

Daga birnin Yamai abokin aikimu, Mamane Ada ya turo mana da wannan rahoto. 

Bisa rahoton ministan kasa, ministan tsare-tsaren yankuna, zaman taron ministoci ya amince da kudurin dage hanin ayyukan jam’iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hulla da makamantansu.

Ta hanyar kuduri mai lamba 2024-02330/PT-MR na ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2024, gwamnatin Mali ta dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hulla da makamantansu.

Manufar yin haka, ita ce ta kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da doka da oda, ganin yadda kasar take fuskantar kalubale da dama, ta fannin tsaro, ta fannin siyasa da na al’umma, domin ganin an shirya taron tattaunawa tsakanin ’yan kasar Mali.

Bisa wannan mataki ne, gwamnatin Mali ta samu dakile dukkan barazana da tabbatar da doka da oda dake da nasaba da tsaron kasa da makomar kasar Mali.

Wannan taron tattaunawa na tsakanin ’yan kasar Mali ya gudana cikin yanayi mai kyau a duk fadin kasar daga ranar 13 ga watan Afrilu zuwa 10 ga watan Mayun shekarar 2024.

Domin aiwatar da shawarwari na taron tattaunawa na tsakanin ’yan kasar Mali da kuma ganin yanayin tsaro ya daidaituwar tsaro, da na siyasa da na al’umma, gwamnatin Mali ta dauki matakin dage dakatarwar da aka ma ayyukan jam’iyyun siyasa da na kungiyoyin fararen hulla da makamantansu.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.