An kaddamar da babban aikin hanyar mota karkashin shirin hadin gwiwar Sin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo
2024-07-11 11:06:16 CMG Hausa
An kaddamar da shirin hadin gwiwar Sin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo, na gyarawa da zamanantar da babbar hanyar mota a kauyen Nguba, dake lardin Lualaba na kudu maso gabashin janhuriyar dimokaradiyyar Congo.
Yayin gagarumin bikin kaddamar da aikin na babbar hanyar “N1”, da zai hade yankunan Mbuji da Mayi-Nguba wanda ya gudana a jiya Laraba, karamin ministan ma’aikatar samar da ababen more rayuwa da ayyukan al’umma na kasar Alexis Gisaro Muvuni, ya tuka motar hakar kasa domin alamta bude aikin.
Mista Muvuni, ya jinjinawa kwarewa da sanin makamar aiki na kamfanin Sin da zai gudanar da aikin, yana mai cewa a baya bayan nan an kaddamar ayyuka da dama, na samar da ababen more rayuwa karkashin hadin gwiwar Sin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo, ciki har da babbar hanyar sha-tale-tale ta birnin Kinshasa, ayyukan da za su yi matukar tallafawa rayuwar mazauna wuraren. (Saminu Alhassan)