logo

HAUSA

Abubuwan lura 5 game da gasar cin kofin “Copa America” bayan kammala wasannin kusa da kusan na karshe

2024-07-11 21:22:17 CMG Hausa

Rashin nasarar Brazil

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Brazil ta yi fatan “Copa America” zai zamo damar farfadowar ta, bayan ta yi rashin nasara a wasannin ta na farko na neman gurbin buga gasar cin kofin duniya na 2026. Amma maimakon hakan, sai abubuwa suka kara tabarbarewa ga kungiyar duk da ta taba yin nasarar lashe kofin kwallon kafa na duniya har karo 5 a baya.

Duk da cewa masu tsaron bayan kungiyar sun taka rawar gani, amma zura kwallo a raga ya gagara, ga kuma tauraron ta Neymar a zaune yana kallo, saboda rauni da yake da shi da ya hana shi bugawa kungiyar ta sa wasa.

Baya ga wasan da Brazil din ta ci Paraguay 4 da 1, ‘yan wasan karkashin koci Dorival Junior, kwallo daya tak suka iya ci a sauran wasannin da suka buga guda 3.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan wasan na Brazil na da sabani da koci Dorival, tun kafin wasan da suka yi nasara kan Uruguay, lamarin da ake ganin zai iya shafar makomar kocin a kungiyar.

Rodriguez ya ingiza Colombia zuwa sabon matsayi

Duk da yadda yake samun koma baya a wasannin da yake bugawa kulaf din sa na São Paulo dake Brazil, tauraron kwallon kafa na Colombia James Rodriguez yana haskakawa sosai a wasannin da yake bugawa Colombia.

Dan wasan mai shekaru 32 a duniya, wanda kuma ke neman sabon kulaf bayan rashin tabuka wani abun azo a gani a tsawon watanni 12 da ya yi a Sao Paulo, a wasannin nan na “Copa America” ya ci kwallo daya, tare da taimakawa a ci kwallaye har 5 cikin wasanni 4 na farko da Colombia ta buga. Hakan na zuwa ne yayin da ‘yan wasan kungiyar ke ta kokarin lashe kofin na “Copa America” a karo na biyu karkashin jagorancin koci Nestor Lorenzo.

“Yan wasan Colombia masu taka rawar gani a tsakiya sun hada da Richard Rios, da Jhon Arias, da Jefferson Lerma, da kuma Rodriguez, yayin da Jhon Cordoba, da Luis Diaz ke rike da gaban kungiyar wajen kai hare hare.

Kaza lika, ‘yan wasan na Colombia sun taka rawar gani wajen tsaron gida, inda kawo yanzu kwallo 2 kacal aka jefa musu a raga a wannan gasa, albarkacin hadakar Carlos Cuesta da Davinson Sanchez dake tsakiya.

Uruguay na shirin farfadowa

Ga alama kungiyar Uruguay na shirin farfadowa karkashin kocin ta dan asalin Argentina Marcelo Bielsa, wanda a watan Mayun shekarar 2023 ya maye gurbin Diego Alonso.

Kwazon da Uruguay ta yi a wasannin neman gurbin buga gasar cin kofin duniya daga kudancin Amurka, ya zarce zuwa gasar “Copa America” da kasar ke bugawa a yanzu, inda ‘yan wasan na koci Bielsa suka yi nasara kan Panama, da Bolivia, da Amurka da Brazil.

Yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida, bayan nasarar da kungiyar da yake jagoranta a ranar Asabar ta samu, koci Bielsa wanda ya taba horas da kungiyoyin kasashen Argentina da Chile, ya ce sun shirya sosai domin tinkarar abokan karawa, don haka suka yi nasara kan Brazil. Yanzu dai Uruguay za ta fuskanci Colombia ne a wasa na gaba, da kuma fatan haduwa da Argentina a wasan karshe.

Ba dai wanda zai iya cewa Uruguay ba za ta iya daga wannan kofi na  “Copa America” ba a karo na biyu, tun bayan na farko da ta dauka a shekarar 2011.

Lautaro Martinez na haskakawa a “Copa America”

A dai wannan gasa ta “Copa America”, kungiyar kwallon kafar Argentina ba ta fuskanci matsi sosai ba a wasannin rukuni da ta buga, inda ta yi nasarar doke Canada, da Chile, da Peru ba tare da an zura mata kwallo a raga ba. To sai dai kuma, ‘yan wasan na Argentina karkashin jagorancin koci Lionel Scaloni, sun sha da kyar a wasan kusa da kusan na karshe da suka buga da Ecuador, wanda ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kyaftin din kungiyar Lionel Messi, bai samu haskawa sosai a daukacin gasar ba, inda ya sha fama da mura a wasannin farko na gasar, kafin daga bisani ya yi fama da ciko a cinyarsa, wanda hakan ya sa aka maye gurbinsa da Lautaro Martinez, tun kafin wasan karshen na rukuni da Argentina din ta buga da Peru.

Ya zuwa yanzu, Lautaro Martinez ya ci kwallaye 4 a gasar, inda ya yi gaba da matsayin dan wasa mafi cin kwallaye, kuma tauraruwarsa na kara haskawa a kungiyar.

Dan wasan mai shekaru 26, kuma ‘dan wasan gaban Inter Milan, ya samu damar taka muhimmiyar rawa a wasanni biyu na karshen nan da Argentina ta buga, wanda hakan ya sanya shi mayar da Julian Alvarez na Manchester City teburin jira.

Canada ta yi rawar gani

Kafin bude gasar ta “Copa America”, da yawa daga manazarta gasar ba su yi tsammanin kungiyar kwallon kafa ta Canada za ta yi abun azo a gani ba, har ma wasu na ganin ba za ta wuce zagayen rukuni na gasar ba. To sai dai kungiyar ta baiwa kowa mamaki, inda karkashin jagorancin kocin ta Jesse Marsch, ta yi nasarar zuwa zagayen siri-daya-kwale, kana ta kai ga shiga jerin kungiyoyi 4 na karshen gasar bayan da suka doke Venezuela a wasan kusa da kusan na karshe, ta bugun daka kai sai mai tsaron gida.

Ko da yake a wasan kusa da na karshe, Argentina ta yi nasara kan Canada da ci 2 da nema, a wasan da suka buga a filin wasa na MetLife dake New Jersey a ranar Talata, ana iya cewa Canadan ta yi rawar gani kwarai da gaske a gasar.