Sin na adawa da abubuwan da ke da alaka da ita a cikin sanarwar taron kolin Washington na NATO
2024-07-11 20:15:54 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a taron manema labaru da aka saba gudanarwa a yau Alhamis ranar 11 ga wata cewa, sanarwar taron koli na Washington na kungiyar tsaro ta NATO ta yi karin gishiri kan halin da ake ciki a yankin Asiya da tekun Pasifik, kuma tana cike da tunanin yakin cacar-baka da kalamai masu iya tayar da yaki, kana abubuwan da sanarwar ta alakanta da kasar Sin suna cike da son zuciya, batanci da tsokana, wadanda ba mu yarda da su ba kuma mun nuna matukar takaici game da haka ga NATO.
Kaza lika, jami’in ya nuna cewa, an gudanar da wannan taro ne a daidai lokacin da kungiyar tsaro ta NATO ta cika shekaru 75 da kafuwa, domin nuna wajabcin wanzuwarta, kasar Amurka da NATO sun mayar da ita a matsayin "kungiyar wanzar da zaman lafiya" kafin taron, amma ba za a taba boye gaskiya cewa ta zama tarihi sakamakon yakin cacar baka, da rura wutar adawa da kuma kafa kananan kungiyoyin siyasa da take yi ba.
An ba da rahoton cewa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana a gun dandalin tattaunawa na taron koli na kungiyar tsaro ta NATO a jiya Laraba cewa, a cikin shekara daya da rabi da ya gabata, mun ga yadda kasar Rasha ta samu karin makamai, wanda ya samo asali ne daga taimakon da kasar Sin ke bayarwa ga tushen harkokin tsaron kasar ta Rasha.
Game da wannan batu, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin tana kakkausar adawa da ci gaba da yada labaran karya da Amurka ke yi, na cewa kasar Sin tana goyon bayan masana’antun tsaron kasa na Rasha ba tare da wata shaida ba.
Lin Jian ya sake nanata cewa, maimakon nuna goyon baya ga wani bangare a cikin rikice-rikice, kamata ya yi Amurka ta yi tunani kan musabbabin rikicin, ta kuma yi wani abu mai amfani don tabbatar da zaman lafiya da gaske. (Bilkisu Xin)