logo

HAUSA

Rahotanni biyu sun tabbatar da cewa Philippines kasa ce dake bata muhallin tekun kudancin kasar Sin

2024-07-10 22:18:58 CMG Hausa

Hukumomin kasar Sin sun bullo da wasu muhimman rahotanni biyu kwanan nan, dake kunshe da rahoton binciken muhallin halittun yankin teku na tsibirin Huangyan da aka fitar a yau Laraba, da rahoton bincike kan illolin da jiragen ruwan sojan da aka jibge a karamin tsibirin Ren’ai Jiao ba bisa doka ba suka haifar ga tsarin murjani a kasan teku, wanda aka fitar a ranar 8 ga watan nan. Dukkan rahotannin biyu sun yi nazari sosai kan yanayin muhallin halittun dake tsibirin Huangyan da karamin tsibirin Ren’ai Jiao, tare kuma da gabatar da mabambantan sakamakon dake nuna cewa, muhallin yankin teku na tsibirin Huangyan na cikin aminci, kana, murjani a kasan tekun lafiya kalau yake. Amma akasin haka, an yi babbar illa ga murjani a kasan teku na karamin tsibirin Ren’ai Jiao, saboda tasirin ayyukan da jiragen ruwan sojan Philippines da aka jibge a wurin ba bisa doka ba suka yi.

Kwararan shaidu sun nuna cewa, kasar Philippines ce ke kawo babbar illa ga muhallin halittun tekun kudancin kasar Sin. Abun da ya kamata kasar ta yi shi ne, ta tuba ta gyara kura-kuranta, da kwashe jiragen ruwan sojanta ba tare da bata lokaci ba, domin kawar da asalin gurbatar muhallin wurin, da kauce wa kara illata muhallin halittun wurin na dogon lokaci.

Kiyaye muhallin halittun yankin teku na da alaka sosai da muradun bil’adama, don haka, bai kamata batun tekun kudancin kasar Sin ya zama hanyar da wasu kasashe kalilan suke bi, wajen yin fito-na-fito a yankin da neman cimma muradun kansu ba. (Murtala Zhang)