logo

HAUSA

Lardin yammacin Cape na Afrika ta kudu na fama da ambaliyar ruwa

2024-07-10 10:59:31 CMG Hausa

 

Kafafen yada labarai ta kasar Afrika ta kudu sun ba da labarin cewa, an yi ruwan sama kamar bakin kwarya a lardin yammacin Cape, lamarin da ya sa birane da dama ciki har da Cape Town fama da ambaliyar ruwa, inda dubban magidanta suka rasa gidajensu.

Ambaliyar ruwan ta lalata hanyoyi da gidaje a unguwanni 70 dake sassan birnin, baya ga gine-gine fiye da 7000 da suka lalace.

Hukumar ilmi ta lardin ta labarta a jiya Talata cewa, bala’in ya shafi makarantu 82 dake lardin, ciki har da 31 dake cikin mummunan yanayi, da kuma 5 da ala tilas aka rufe su.

Hukumar binciken yanayi ta kasar ta yi kiyasin cewa, za a ci gaba da samun ruwan sama mai karfi, da mahaukaciyar iska a lardin. A daya bangaren kuma, hukumar bayar da agajin gaggawa ta lardin ta bayyana a jiya cewa, ana kidaya asarar da bala’in ya haddasa, kuma gwamnatin lardin na kokarin tsugunar da mutanen da bala’in ya ritsa da su. (Amina Xu)