logo

HAUSA

An amince da karawa 'yan majalissar wakilan Kamaru wa'adin shekara daya

2024-07-10 11:32:07 CMG Hausa

Majalissar wakilan kasar Kamaru, ta amince da karawa mambobinta wa'adin aiki na shekara guda, wato zuwa ranar 30 ga watan Maris na 2026, maimakon 10 ga watan Maris na shekarar 2025 da ya kamata su kammala wa'adin aikin na su.

Hakan dai ya biyo bayan amincewa da wani kudurin doka ne da aka gabatarwa majalissar ta wakilai. Kuma yayin zaman majalissar na jiya Talata, kakakin ta Cavaye Yeguie Djibril, ya ce karin wa'adin na da matukar muhimmanci ga burin ragen cushewar jadawalin babban zaben kasar na badi, wanda zai kunshi na shugaban kasa, da majalissun dokoki, da kananan hukumomi, da 'yan majalissun yankunan kasar.

A makon jiya ne dai gwamnatin Kamarun ta ce tsawaita wa'adin aikin 'yan majalissar wakilan kasar, zai ba da damar rarraba lokutan zaben kasar tsakanin shekarar 2025 da 2026, ta yadda za a kai ga cimma nasarar gudanar da su bisa kyakkyawan tsari.  (Saminu Alhassan)