Yawan kudaden da al’ummun dake kasar Sin suka kashe a watan Yuni ya karu da kaso 0.2%
2024-07-10 11:20:43 CMG Hausa
Bayanin da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, a watan Yuni na bana, yawan kudaden da mutanen dake kasar Sin suka kashe ya karu da kaso 0.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. A ciki kuma, yawan kudaden da aka kashe a birane ya karu da kaso 0.2 bisa dari, yayin da adadin ya karu da kaso 0.4 bisa dari a yankunan karkarar Sin.
A sa’i daya kuma, farashin abinci ya ragu da kaso 2.1 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara, kuma farashin kayayyakin da ba na abinci ba, ya karu da kaso 0.8 bisa dari. Haka kuma, farashin kayayyakin yau da kullum ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, yayin da farashin samar da hidimomi ya karu da kaso 0.7 bisa dari.
Bugu da kari, a tsakanin watan Janairu da watan Yunin bana, matsakaicin yawan kudaden da mutanen dake kasar Sin suka kashe ya karu da kaso 0.1 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. (Mai Fassara: Maryam Yang)