logo

HAUSA

Ya zuwa shekarar 2023 yawan jama'ar Senegal ya haura miliyan 18

2024-07-10 09:57:42 CMG Hausa

Alkaluman da hukumar kididdiga da tantance bayanai kan hakan ta kasar Senegal ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa shekarar 2023 da ta gabata, adadin yawan jama'ar kasar ya karu zuwa mutum 18,126,390.

Hukumar wadda ta fitar da alkaluman a jiya Talata, cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, mai kunshe da takaitattun alkaluman babbar kidaya ta 5 ta al'umma da gidajen kasar, ta ce cikin jimillar al'ummar Senegal, kusan kaso 50.6 bisa dari maza ne, yayin da kaso 49.4 bisa dari kuma mata ne. Har ila yau, adadin matasa dake kasa da shekaru 35 ya kai kaso 75 bisa dari, kuma cikin wannan adadin kusan rabi 'yan kasa da shekaru 19 ne, kana kaso 39 bisa dari 'yan kasa da shekaru 15 ne.

Alkaluman da hukumar ta fitar sun kuma nuna cewa, tsakanin shekarar 2013 da 2023, adadin jama'ar kasar sun rika karuwa da kaso 2.9 bisa dari a duk shekara, kuma a kan wannan mizani cikin shekaru 25 masu zuwa, yawan al'ummar kasar zai ninka na yanzu.

Kaza lika, karuwar jama'ar Senegal ta fi yawa a birane, inda aka samu karuwar kaso 54.7 bisa dari, musamman a yankunan biranen Dakar, da Thies da Diourbel, wadanda ke da kaso 47 bisa dari na daukacin al'ummar kasar.  (Saminu Alhassan)