logo

HAUSA

Vladimir Putin da Narendra Modi sun tattauna kan rikicin Ukraine da sauran bututuwa

2024-07-10 10:50:12 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya tattauna da firaministan Indiya Narendra Damodardas Modi a fadar Kremlin, kan huldar kasashen biyu da rikicin Ukraine da sauransu. Mista Modi ya gudanar da ziyarar aiki a Rasha ne a ranekun Litinin da Talata, kuma wannan ne karon farko a cikin shekaru 5 da suka gabata da ya ziyarci kasar Rasha.

Bisa labarin da shafin yanar gizo na fadar Kremlin ya fitar, an ce, yayin tattaunawarsu, shugaba Putin ya ce bangarorin biyu na gudanar da hadin kai yadda ya kamata a fannin raya tattalin arziki da cinikayya, kuma suna hadin gwiwa a harkokin duniya karkashin tsarin MDD, da BRICS, da SCO da sauransu.

A nasa bangare, Modi ya ce, kasarsa ta gamsu da bukatar warware rikicin Ukraine cikin lumana, da fatan ba da taimakon ta.(Amina Xu)